Taron Farko Na Hukumar Yan Sanda Ta Tarayyar Afrika AFRIPOL A Algeria
An bude taron hukumar yan sanda ta tarayyar Afrika AFRIPOL a takaice a birnin Algiest na kasar Algeria, tare da halattar shuwagabannin yan sanda na kasashen nahiyar Afrika da wasu kasashen duniya.
Taron na kwanaki uku wato daga 14-16 ga watan mayu da muke ciki ya sami halattar wakilai daga kasashe 25 na kasashen Afrika, kuma sun fara tattauna batun dokokin da za su tafiyar da wannan sabuwar hukuma, zabe ko kuma nada shuwagabannin komitoci daban daban da za su kafa a wannan taro, har'ila yau a taron ne zasu fayyace yadda yan sandan wadannan kasashe za su yi aiki tare a fagen cikin gida, nahiyar da kuma kasa da kasa.
Major-general Abdul-ghani Hamil hukumar ma'aikatar tsaro na kasar Algeria ya bayyana cewa cibiyar rundunar yansanda ta AFRIPOL zai kasance a birnin Algiest na kasar Algeria. Sannan kafa rundunar AFRIPOL zai taimaka wajen ganin kasashen Afrika zasu fito a tsakanin kasashen duniya da murya guda kan abinda ya shafi harkokin tsaro a nahiyar da ma kasa da kasa.
Hamil ya kara da cewa rundunar yansanda ta AFRIPOL zata taka rawa wajen tabbatar da tsaro a da zaman lafiyar a cikin nahiyar Afrika musamman a bangaren yaki da ayyukan ta'addanci wanda a halin yanzu ya addabi mafi yawan kasashen nahiyar.
A taron shuwagabannin Afrika karo na 28 wanda aka gudanar a karshen watan Jenerun wannan shekara ne shuwagabannain suka amince da kafa rundunar AFRIPOL . A taron na birnin Algiest ne ake saran za'a kafa babban majalisar gudanar da rundunar ta AFRIPOL da kuma yadda zata gudanar da ayyukanta na tabbatar da tsaro na nahiyar.
Tabbatar da tsaro da kuma yaki da ayyukan ta'addancin su ne muhimman lamuran da AFRIPOL zata fara aiki a kansu. Yaki da kungiyoyin yan ta'adda wadanda suka hada da Boko Haram wacce yake aiwatar da ayyukan ta'addanci a tarayyar Nigeria da kuma makobtanta Kamaro da Chadi da Niger. Har'ila yau da kungiyar Alshaba wacce ta hana zaman lafiya a kasar Somalia da makobtanta na shekaru masu yawa duk duna daga cikin Agendan rundunar AFRIPOL .
Banda haka a arewacin Afrika rashin zaman lafiya a kasar Libya ya haifar da mummunan tasiri a kasar da kuma kasashe makobta wadabda suka hada da Masar Tunisia da kuma ita ALgeria. Wadannan matsalolin tsaro dai dun shafi harkokin siyasa tattalin arziki zamantakewa da kuma cigaban nahiyar Afrika gaba daya.
Sai kuma katsalandar kasashen yamma a cikin al-amuran cikin gida na kasashen nahiyar Afrika, da sunan taimaka masu wajen yakar ayyukan ta'addanci da kuma tabbatar da zaman lafiya a kasashen nahiyar ya kara rikita lamuran tsaro a cikinsu. Don haka batun cire hannun kasashen yamma a cikin lamuran tsaro a kasashen nahiyar Afrika na daga cikin muhimman ayyukan rundunar AFRIPOL idan aikinta ya kankama.
A halim yamzu dai masana suna ganin kafa rundunar AFRIPOL shi ne mataki na farko wajen warware matsalolin tsaro na nahiyar Afrika da kuma samun damar aiwatar da siyasar bai daya a duk fadin nahiyar . Har'ila yau ana saran rundunar zata zama wata kofa ta hana kan kasashen yankin wajen yakar ayyukan ta'addanci a duk fadin nahiyar ta Afrika.