Sace Wasu Ma'aikatan Kungiyar Red Cross Guda 4 A Kasar Mali
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i20434-sace_wasu_ma'aikatan_kungiyar_red_cross_guda_4_a_kasar_mali
Kungiyar bada agajin gaggawa ta kasa da kasa ta Red Cross ta sanar da sace wasu ma'aikatanta guda hudu a kasar Mali.
(last modified 2018-08-22T11:30:07+00:00 )
May 16, 2017 12:15 UTC
  • Sace Wasu Ma'aikatan Kungiyar Red Cross Guda 4 A Kasar Mali

Kungiyar bada agajin gaggawa ta kasa da kasa ta Red Cross ta sanar da sace wasu ma'aikatanta guda hudu a kasar Mali.

Majiyar kungiyar bada agajin gaggawa ta kasa da kasa ta Red Cross a kasar Mali ta sanar da cewa: Wasu gungun 'yan bindiga sun sace ma'aikatan kungiyar ta Red Cross guda 4 a yammacin ranar Lahadin da ta gabata a yankin Tenekou da ke gundumar Mopti a tsakiyar kasar Mali.

Majiyar ta kara da cewa: 'Yan bindigan sun yi awungaba da ma'aikatan ne a lokacin da suke gudanar da bincike kan harkokin jin kai a yankin.

Wasu magabatan yankin sun bayyana cewa: 'Yan bindiga masu tsaurin ra'ayin kishin Islama ne suka sace ma'aikatan na Red Cross, kuma a halin yanzu haka an fara neman hanyar tuntubarsu domin ganin sun saki ma'aikatan da suka yi garkuwa da su.