An Hallaka Daya Daga Cikin Komondojin Kungiyar Boko Haram A Najeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i20466-an_hallaka_daya_daga_cikin_komondojin_kungiyar_boko_haram_a_najeriya
Magabatan tsaron kamaru sun sanar da hallaka wani komandan kungiyar Boko haram tare da rusa maboyar su a garin Banki na Najeriya.
(last modified 2018-08-22T07:00:07+00:00 )
May 17, 2017 14:21 UTC
  • An Hallaka Daya Daga Cikin Komondojin Kungiyar Boko Haram A Najeriya

Magabatan tsaron kamaru sun sanar da hallaka wani komandan kungiyar Boko haram tare da rusa maboyar su a garin Banki na Najeriya.

Kafar watsa labaran Afirka Time ta nakalto jami'an tsaron kasar Kamaru na cewa daya daga cikin komondojin kungiyar boko haram mai suna Abdu Nasif ya hallaka a jiya Talata bayan wani sumame da Sojojin kasar Kamaru dake aiki kalkashin rundunar hadin gwiwa na kasashen dake yaki da kungiyar boko haram suka kai a garin Banki dake cikin Nijeriya kusa da kan iyakar kasar Kamaru.

Jami'an tsaron kasar ta Kamaru sun ce Abdu Nasif ya hallaka ne a yayin musayar wuta tsakanin mayakan na Boko haram da Sojojin kasar Kamaru dake samun goyon bayan Dakarun Najeriya.

A shekarar 2015 ne dai kasashen Najeriya, Nijer, Kamaru da Tchadi suka kafa Rundunar hadin gwiwa domin yakar kungiyar boko haram dake hare-haren ta'addanci a kasashen na su.a nata bangare rundunar tsaron kasar Kamaru na ci gaba da tsare kan iyakokin arewacin kasar dake da iyaka da Najeriya da nufin hana mayakan kungiyar boko haram samun gindin zama a kasar ta Kamaru.