Tsohon Shugaban Kasar Senegal Zai Tsaya Takarar Majalisar Dokokin Kasa
(last modified Wed, 31 May 2017 17:33:36 GMT )
May 31, 2017 17:33 UTC
  • Tsohon Shugaban Kasar Senegal Zai Tsaya Takarar Majalisar Dokokin Kasa

A daidai lokacin da zaben 'yan majalisar kasar Senegal ke ci gaba da kusatowa, an bayyana cewar tsohon shugaban kasar Abdoulaye Wade na shirin tsayawa takara zama dan majalisar wakilan kasar.

Rahotanni sun ce matakin tsayawa takara a zaben 'yan majalisar da tsohon shugaban Wade ya dauka ya biyo bayan rugujewar hadaka ta sama da jam'iyyun siyasa 40 ta 'yan adawar kasar ne sakamakon sabanin ra'ayi da aka samu tsakanin magoya bayan shugaba Wade da daya daga cikin madugun 'yan adawan kuma magajin garin Dakar Khalifa Sall kan wanda zai jagoranci 'yan takarar hadakar.

Jam'iyyun adawar sun kulla wannan hadakar ce da nufin samun rinjaye a majalisar lamarin da zai tilasta wa shugaban kasar Macky Sall raba madafun iko da 'yan adawan.

Shugaba Abdoulaye  Wadem dan shekaru 91 a duniya ya shugabanci kasar ta Senegal din ne har na tsawon shekaru 12 wato daga shekarar 2000 zuwa 2012 kafin ya sha kaye a zaben shugaban kasar da aka gudanar a shekara ta 2012 inda shugaba mai ci ga Macky Sall ya kada shi.