Sojojin Tunisia Sun Yi Musayar Wuta Da 'Yan Ta'adda A Yammacin Kasar
Jami'an sojin kasar Tunisia sun yi musayar wuta mai tsanani tare da 'yan ta'addan takfiriyya a yankunan yammacin kasar.
Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa ya bayar da rahoton cewa, a jiya kakakin ma'aikatar harkokin cikin gida a kasar Tunisia Bilhasan Alwuslati ya bayyana cewa, dakarun kasar sun kaddamar da farmaki a wata maboyar 'yan ta'adda a yankin Jabal Samamah da ke cikin gundumar Qasrain.
Ya kara da cewa an yi musayar wuta tsakanin dakarun na Tunisia da kuma 'yan ta'addan, inda aka kashe wani babban kwamandan 'yan ta'addan tare da kame wasu, kamar yadda kuma aka samu tarin makamai a maboyar tasu.
Kasar Tunisia dai tana a matsayin kasa ta biyu bayan Saudiyyah, wajen yawan 'yan ta'addan da suke yaki a kasashen Syria da Iraki a sahun mayakan ISIS.