Ana Ci Gaba Da Kokarin Warware Rikicin Kasar Libya Ta Hanyar Tattaunawa
Priministan rikon kwarya na gwamnatin hadin kan kasar libya ya tattauna da tawagar tarayyar Afrika ta musamman kan yadda za'a warware rikicin kasar ta hanyar tattaunawa.
Kamfanin dillancin labaran Chinhuwa na kasar China ya nakalto tawagar tarayyar Afrikan tana fanar haka a safiyar yau Alhamis bayan ganawarta da Fa
ez Suraj Priministan gwamnatin hadin kan kasar da Libya. Tawagar tarayyar Afrikan dai ta hada da ministocin harkokin wajen kasashen Congo Brazaville, Guinea, Niger, Mauritania da kuma Isma'ila Sharqawi jami'i a sashen tsaro da sulhu na kungiyar Tarayyar Afrika. Tawagar ta bayyana goyon bayanta ga Priministan kasar ta Libya kan tattaunawa da dukkan bangarin yan siyasar kasar Libya don kaiwa ga zaman lafiya a kasar.
A nashi bangaren Fa'ez Suraaj Priministan rikon gwamnatin hadin kan kasa ya godewa tawagar tarayyar Afrika kan ziyarar da suka kawo kasar don bada gudumawa wajen ganin kasar Libya ta fita cikin dimbin matsalolin tsaro da ta fada ciki, ya kuma kara da cewa kasar Libya ba zata fita cikin wadan nan matsaloli ba sai lokacinda kasashen waje suka dai shiga cikin harkokin kasar.