Gwamnatocin Sudan Da Chadi Sun Kulla Yarjejeniyar Komawar 'Yan Gudun Hijira Kasarsu
(last modified Thu, 01 Jun 2017 19:22:52 GMT )
Jun 01, 2017 19:22 UTC
  • Gwamnatocin Sudan Da Chadi Sun Kulla Yarjejeniyar Komawar 'Yan Gudun Hijira Kasarsu

Gwamnatin Sudan da Chadi sun rattaba hannu kan yarjejeniyar komawar 'yan gudun hijira zuwa kasashensu bisa radin kansu.

Gwamnatocin Sudan da Chadi da kuma Hukumar Kolin Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya a yau Alhamis sun rattaba hannu kan yarjejeniyar komawar 'yan gudun hijirar kasashen biyu zuwa muhallinsu da tashe-tashen hankula suka raba su da shi.

A karkashin yarjejeniyar an jaddada wajabcin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da yankunan da 'yan gudun hijirar zasu koma domin ci gaba da gudanar da rayuwarsu tare da wadata su da kayayyakin bukatu na yau da kullum.

Tun bayan bullar yakin basasa a yankin Darfur da ke yammacin kasar Sudan a shekara ta 2003 dubban daruruwan 'yan Sudan suka tsallaka kan iyakar kasar Chadi domin neman mafaka, inda aka tsugunar da su a sansanoni daban daban, kuma har yanzu haka akwai 'yan gudun hijirar ta Sudan a kasar Chadi da suka doshi dubu tamanin.