An Jikkata Sojojin Faransa A Mali
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i20940-an_jikkata_sojojin_faransa_a_mali
Dakarun tsaron Faransa dake kasar Mali sun sanar a jiya Alkhamis cewa wasu daga cikin Sojojin su takwas sun jikkata sanadiyar Harin da aka kai sansanin Dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD a garin Tunbuctou dake kasar ta Mali.
(last modified 2018-08-22T11:30:11+00:00 )
Jun 02, 2017 06:39 UTC
  • An Jikkata Sojojin Faransa A Mali

Dakarun tsaron Faransa dake kasar Mali sun sanar a jiya Alkhamis cewa wasu daga cikin Sojojin su takwas sun jikkata sanadiyar Harin da aka kai sansanin Dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD a garin Tunbuctou dake kasar ta Mali.

Rundunar sojojin Mali ta sanar da mutuwar sojojinta guda uku, sannan kuma wasu sojojin kasar Faransa guda takwas sun samu raunuka sakamakon wani harin ta'addanci.

Lamarin ya faru ne ne da misalin  karfe takwas da minti 40 ne na Safiyar jiya Alkhamis ne agogon kasar ta Mali,  a sansanin dakarun Majalisar Dinkin Duniya na MINISMA da ke birnin Tombouctou a cewar mai magana da yawun dakarun sojojin kasar Faransa Kanal Patrik Steiger, wanda ya ce daya daga cikin sojoji takwas na Faransa da suka ji ciwo na cikin mawuyacin hali.

Daga nata bangare rundunar sojojin kasar ta Mali cikin wata sanarwa, ta ce maharan sun halba wani babban makami ne a filin sauka da tashi na jiragen sama na  garin Tombouctou.

A daren Larabar da ta gabata ma, wasu  gungun 'yan bindiga kan babura sun kaddamar da harin wuce gona da iri kan jami'an tsaron kasar Niger a garin Abala da ke Jihar Tilaberi kusa da kan iyaka da kasar Mali, inda suka kashe jami'an tsaron Niger shida.