Yawan Asarar Rayuka A Arewacin Kasar Mali Ya Karu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i21216-yawan_asarar_rayuka_a_arewacin_kasar_mali_ya_karu
Majalisar dinkin duniya ta bada sanarwan gano karin gawar wani sojojanta a arewacin kasar bayan hare haren da aka kai masu a daren Alhamis da ta gabata
(last modified 2018-08-22T07:00:14+00:00 )
Jun 11, 2017 02:14 UTC
  • Yawan Asarar Rayuka A Arewacin Kasar Mali Ya Karu

Majalisar dinkin duniya ta bada sanarwan gano karin gawar wani sojojanta a arewacin kasar bayan hare haren da aka kai masu a daren Alhamis da ta gabata

Majiyar muryar jumhuriyar musulunci ta Iran daga birnin Bamako babban birnin kasar Mali ya nakalci rundunar dawo da zaman lafiya ta majalisar dinkin duniya a arewacin kasar tana cewa, bayan hare haren da wata kungiyar yan ta'adda wacce take da dangantaka da kungiyar Alqaeda ta kaiwa sojojin rundunar a birnin Kidal a daren ranar Alhamis da ta gabata, yawan sojojin da suka rasa rayukansu ya karu daga ukku zuwa hudu bayan an gani wani karin gawan sojon rundunar.

Duk da cewa shekara guda kenan da rattaba hannu kan yerjejeniyar sulhu tsakanin gwamnatin kasar Mali da mafi yawan yan tawayen kasar amma har yanzun an kasa samun zaman lafiya a yankin. 

Wasu masana suna ganin shigar sojojin kasar Faransa cikin rikicin kasar ta Mali da kuma samuwar sojojin Majalisar dinkin duniya a arewacin kasar suna daga cikin abubuwan da suka hana rikicin kasar lafawa.