An Saki Saiful Islam Dan Tsohon Shugaban Kasar Liya Daga Kurkuku
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i21218-an_saki_saiful_islam_dan_tsohon_shugaban_kasar_liya_daga_kurkuku
Kafafen yada labarai na kasashen Larabawa da dama sun bada labarin cewa Saiful Islam dan tsohon shugaban kasar libya ya kubuta daga hannun wadanda suke tsare da shi a garin zantan yammacin birnin Tripoli.
(last modified 2018-08-22T07:00:14+00:00 )
Jun 11, 2017 02:15 UTC
  • An Saki Saiful Islam Dan Tsohon Shugaban Kasar Liya Daga Kurkuku

Kafafen yada labarai na kasashen Larabawa da dama sun bada labarin cewa Saiful Islam dan tsohon shugaban kasar libya ya kubuta daga hannun wadanda suke tsare da shi a garin zantan yammacin birnin Tripoli.

Tashar television ta Al-Alam mai watsa shirye shiryensa da harshen larabci a nan Tehran ya nakalto Skynews arabia tana fadin cewa an saki Saiful Islam ne tare da umurnin gwamnatin kasar, sannan a halin yanzu ba wanda ya san inda ya nufa. 

Labarin ya kara da cewa sakin Saiful Islam ya zo ne bayan da majalisar dokokin kasar ta Libya ta bada umurnin sakin dukkan fursinonin da ake tsare da su na tare da an tabbatar da laifin da suka aikata ba.

Wata kungiyar yan tawaye ce ta ke tsare da Saiful Islam a birnin Zantan tun shekara ta 2011 bayan da suka tsare hanyarsa ta fila kasar daga kudancin kasar ta libya.