Adadin Mutane Da Suka Rasu Sanadiyar Harin Ta'addanci A Mali Ya Karu
Jun 11, 2017 07:43 UTC
MDD ta gano wasu gawawarki hudu na dakarunta a arewacin kasar Mali
A cikin wata Sanarwa da ta fitar MDD ta ce harin ta'addancin da aka kaiwa Dakarunta a daren Alkhamis din da ta gabata a birnin Kidal dake arewacin kasar Mali yayi sanadiyar mutuwar mutane 8.
Jim kadan bayan kai harin, wata kungiya mai alaka da kungiyar Alka'ida ta dauki nauyin kai harin.
bayan kwashe sama da shekara guda da cimma yarjejjeniyar Sulhu tsakanin Gwamnatin Mali da kungiyoyin 'yan tawayen kasar, har yanzu kasar na fuskantar matsalar rashin tsaro.
Duk da shigar Dakarun kasar Faransa bisa da'awar yaki da ta'addanci da kuma Dakarun MDD, hakan ya kasa tasiri wajen warware rikicin arewacin kasar ta Mali.
Tags