Antoni Janar Na Libiya: Sake Saiful Islam Ghaddafi Ya Saba Wa Doka
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i21300-antoni_janar_na_libiya_sake_saiful_islam_ghaddafi_ya_saba_wa_doka
Antoni Janar kuma babban mai shigar da kara na kasar Libiya Ibrahim Masoud Ali ya bayyana cewar sake dan tsohon shugaban kasar Libiya, Mu'ammar Ghaddafi, wato Saiful Islam Ghaddafi daga gidan yari da aka yi ya saba wa dokokin kasar inda ya bukaci da a sake kama shi.
(last modified 2018-08-22T07:00:14+00:00 )
Jun 14, 2017 01:00 UTC
  • Antoni Janar Na Libiya: Sake Saiful Islam Ghaddafi Ya Saba Wa Doka

Antoni Janar kuma babban mai shigar da kara na kasar Libiya Ibrahim Masoud Ali ya bayyana cewar sake dan tsohon shugaban kasar Libiya, Mu'ammar Ghaddafi, wato Saiful Islam Ghaddafi daga gidan yari da aka yi ya saba wa dokokin kasar inda ya bukaci da a sake kama shi.

Rahotanni daga kasar Libiyan sun ce  Antoni Janar din ya bayyana hakan ne a yayin da yake bayyana matsayar Ma'aikatar shari'a ta kasar Libiyan inda ya ce sake Saiful Islam Ghaddafi da aka yi daga gidan yari wani lamari ne da ya saba wa dokokin kasar don haka sai ya bukaci da a sake kamo shi da ci gaba da tsare shi.

Babban mai shigar da karar ya ci gaba da cewa hatta bisa afuwar da aka ce an yi wa jami'an tsohuwar gwamnatin Libiyan, akwai bukatar amincewar iyalan wadanda aka cutar, baya ga cewa kotun ICC mai shari'ar manyan laifuffuka tana neman Saiful Islam din bisa zargin aikata laifuffukan yaki. Don haka wajibi ne a kamo shi da gurfanar da shi a gaban kotu.

A ranar Asabar din da ta gabata ce dai mayakan sa kai da suke kiran kansu dakarun "Abubakar Al-Siddiq" wadanda suke rike da Saiful Islam din suka sanar da sake shi bisa dokar afuwa da majalisar kasar mai mazauni a Gabashi ta yi wa jami'an tsohuwar gwamnatin ta Libiya.