Majalisar Dinkin Duniya Ta Zabi Sabon Jakadanta Na Musamman A Kasar Libya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i21392-majalisar_dinkin_duniya_ta_zabi_sabon_jakadanta_na_musamman_a_kasar_libya
António Guterres babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya a yau Asabar ya nada sabon jakadan Majalisar a kasar Libya.
(last modified 2018-08-22T11:30:15+00:00 )
Jun 17, 2017 19:15 UTC
  • Majalisar Dinkin Duniya Ta Zabi Sabon Jakadanta Na Musamman A Kasar Libya

António Guterres babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya a yau Asabar ya nada sabon jakadan Majalisar a kasar Libya.

Kamfanin dillancin Labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto wannan labarin daga sanarwan da ofishin babban sakataren ya fitar a yau Asabar, inda sanarwan ya kara da cewa António Guterres ya zabi Gassan Salama dan kasar Lebanon ya maye gurbin Mateen Cobler wanda ya rike wannan mokamin tun shekara ta 2015. 

Bayanin ya kara da cewa babban sakataren ya zabi Salama ne cikin yan takarar neman wannan mukami su 4 da aka gabatar masa don cike gurbin Cobler.

Gassan Salama shi ne jakadan majalisar na ukku tun lokacinda aka fara yakin basasa a kasar libya bayan kifar da gwamnatin Mo'amma Kazzafi a shekara ta 2011.

António Guterres ya nada Gassan Salama kan wannan mukamin ne a dai dai lokacinda kungiyoyin da basa ga maciji a kasar ta Libya suke ta fafatawa a tsakaninsu.