An Kaiwa Sojojin Mali Hari
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i21398-an_kaiwa_sojojin_mali_hari
Wasu 'Yan bindiga sun kai hari Sansanin Sojin kasar Mali dake arewacin kasar , lamarin da yayi sanadiyar mutuwar Sojoji biyar tare da jikkata wasu takwas na daban
(last modified 2018-08-22T11:30:15+00:00 )
Jun 18, 2017 05:44 UTC
  • An Kaiwa Sojojin Mali Hari

Wasu 'Yan bindiga sun kai hari Sansanin Sojin kasar Mali dake arewacin kasar , lamarin da yayi sanadiyar mutuwar Sojoji biyar tare da jikkata wasu takwas na daban

Rahotanni dake fitowa daga kasar Mali sun habarta cewa a safiyar jjiya Assabar wasu 'yan bindiga da ba akai ga gane ko su waye ba sun kai harin kan Dakarun tsaron kasar a barikinsu  na garin Bintagoungou dake arewacin kasar., lamarin da yayi sanadiyar mutuwar Sojoji 5 tare da jikkata wasu 8 na daban

Rahoton ya ce an  kai harin ne da misalin karfe biyar na asubahin jiya  Asabar, kuma maharan sun lalata illahirin kayan aikin sojojin gwamnatin da ke a cikin wannan barikin soja da ke a nisan kilomita 80 da birnin Tombouctou daya daga cikin manyan biranen yankin Arewacin kasar. 

Wasu shaidun gani da ido a garin na Bintagoungou sun ce maharan sun kwashi ganimar kayan yaki mai yawa kana sun kama wasu sojojin sun tafi da su.