Harin Ta'addancin Kungiyar AShabab A Somaliya
(last modified Tue, 20 Jun 2017 18:08:19 GMT )
Jun 20, 2017 18:08 UTC
  • Harin Ta'addancin Kungiyar AShabab A Somaliya

Akalla Mutane 10 ne suka hallaka yayin da wasu da dama na daban suka ji rauni yayin wani harin ta'addanci da kungiyar Ashabab ta kai Magdushu babban birnin kasar Somaliya

Kamfanin dillancin Labaran kasar Faransa ya nakalto Ahmad Mahmoud Mohammad Kakakin Ma'aikatar tsaron Somaliya na cewa wani dan kunar bakin wake na kungiyar Ashabab ya kutsa da mota shake da bama-bamai cikin ginin ma'aikatar Magajin garin yankin Wadajir dake kudancin Magadushu a wannan Talata, lamarin da yayi sanadiyar mutuwar mutane 10 tare da jikkata wasu 9 na daban.

Kakakin Ma'aikatar tsaron Somaliya ya kara da cewa mafi yawa daga cikin wadannan suka rasa rayukansu fararen hula ne da suka je ma'aikatar domin neman wasu takardu.

Kimanin Shekaru 25 kenan da kasar Somaliyan ke fuskantar hare-haren ta'addanci na kungiyar Ashabab.kafin hakan dai, Kungiyar ta Ashabab na ta mamaye wani bangare a tsakiya da kuma kudancin kasar, saidai a 'yan shekarun nan, Dakarun tsaron kasar tare da taimakon Dakarun kasashen Afirka sun kwace mafi yawan gariruwan, abinda ya yi saura hanun kungiyar bai wuce wasu kauyuka dake kudancin kasar ba.