An Kai Harin Kunar Bakin Wake A Arewa Maso Gabashin Najeriya
Akalla mutum 20 ne suka suka rasa rayukansu bayan da wasu 'yan kunar bakin wake suka tarwatsa bama-baman da ke jikinsu a Jami'ar Maiduguri da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto kakakin 'yan sandar jihar Borno na cewa akalla mutane 16 suka rasa rayukansu yayin da wasu 13 na daban suka jikkata sanadiyar harin kunar bakin wake da wasu mahara suka kai jami'ar birnin Maiduguri babban birnin jihar Borno dake shiyar arewa masa gabashin Najiya a wannan Lahadi .
har ila yau ,harin ya yi sanadiyyar mutuwar maharan da ma wata ma'aikaciyar Jami'ar.
Kakakin Jami'ar Farfesa Danjuma Gambo ya shaida wa manema labarai cewa maharan sun tashi bama-baman ne a wuri uku.
"Mace ta farko ta tunkari jami'an tsaron da ke aiki a jami'ar ne inda ta tayar da bam din da ke jikinta. Daya daga cikin jami'an tsaron ta mutu sannan an kai uku asibiti. Ta biyu kuma ta shigo ta gabashin Jami'ar amma jami'an tsaro suka gan ta, nan take suka harbe ta. Bam na uku kuma ya tashi ne a can nesa da jami'ar don haka ba mu sani ba ko mace ce ko namji suka yi yunkurin kai harin".