Wani Matashi Ya Bunkawa Kansa Wuta Saboda Matsalolin Rayuwa A Kasar Libiya
Wani matashi dan shekara 28 a duniya ya bunka wa kansa wuta domin bayyana rashin amincewarsa da irin halin kuncin rayuwar da yake ciki a kasar Libiya.
Majiyar asibiti a kasar Libiya ta sanar da cewa: Wani matashi da ake masa lakabi da Abu-Qasim dan shekaru 28 a duniya ya zo kan shataletale da ke tsakiyar birnin Tripoli fadar mulkin kasar Libiya a yau Talata, inda ya zuba fetur a jikinsa tare da bunka wuta wa kansa domin nuna rashin amincewarsa kan irin mummunan kuncin rayuwa da yake ciki na talauci da rashin aikin yi a kasar.
Hotunan bidiyo da jama'a suka dauka a wayarsu ta salula a lokacin da matashin ke cin wuta, an ga wani matashi na daban ya kai masa dauki yana kokarin kashe masa wutan, inda ya tseratar da shi daga halaka amma yayi mummunan konewa a duk jikinsa.
Tun bayan da kasashen yammacin Turai da Amurka suka ingiza al'ummar Libiya suka yi bore wa shugaban kasar Mu'ammar Gaddafi dan kama karya tare da kawo karshen mulkinsa a shekara ta 2011 wata sabuwar masifa ta kunno kai a kasar na rashin zaman lafiya da kwnciyar hankali lamarin da ya wurga al'ummar Libiya cikin mawuyacin hali a fagen rayuwa.