An Gano Wasu Gawawwakin Bakin Haure A Tekun Libiya
A ci gaba da matsalar bakin haure, an gano wasu karin gawawwaki 25 na bakin haure a tekun kasar Libiya
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto kungiyar Agajin gaggauwa ta kasar Libiya na cewa a jiya Talata sun gano tare da fitar da wasu karin gawawwaki 25 na bakin haure masu kokarin zuwa kasashen Turai a gabar ruwan gabashin Tripoli babban birnin kasar.
Kafin hakan dai, Dakarun tsaron ruwan Libiya sun sanar da ceto bakin haure 147 daga cikin su akwai Mata 19 da kananen yara 4 a kusa da birnin Misrata dake yammacin kasar, Abu Kasim mai magana da yawun Dakarun tsaron ruwan na Libiya ya ce mafi yawa daga cikin Mutanan da aka ceto matasa ne kuma sun fito ne daga kasashen Kamaru, Sudan, Senegal da kuma Mali.
A bangare guda, Jami'an kasar Italiya sun sanar da cewa cikin sa'o'i 48 da suka gabata sun ceto bakin haure sama da dubu takwas a tekun Bahrum. alkaluman da Ma'aikatar cikin gidan Italiyan ta fitar ya ce daga farkon wannan shekara ta 2017 da muke ciki zuwa yanzu bakin haure dubu 73 da dari uku ne suka shiga cikin kasar.