Sojoji 44 Sun Hallaka Cikin Wata Guda Kacal A Bangazi.
Cikin wata guda na gumurzu tsakanin Dakarun tsaron Libiya da 'yan ta'addar ISIS, Sojoji 44 suka rasa rayukansu a binrnin Bangazi dake arewa maso gabashin kasar
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya na nakalto Hani Al-arabie mai magana da yawun Ma'aikatar lafiyar Gwamnatin Libiya dake gabashin kasar na cewa, Sojoji 44 sun rasa rayukansu a fafatawar da aka yi a anguwanin Assabiri da Sukul-hut dake a matsayin karshen tungar 'yan ta'addar ISIS a birnin Bangazi.
Babban Hafsan Sojin kasar ta Libiya ya bukaci Dakarun sa da su kara kaimi wajen kakkabe 'yan ta'addar ISIS da kuma tsarkake birnin Bangazi baki daya daga mamayen 'yan ta'addar Da'esh a cikin wannan maku.
Kimanin watanni uku kenan da sojojin Libiyan karkashin jagorancin Janar Khalifa Haftar suke kai farmaki kan 'yan ta'addar ISIS a Bangazi da nufin tsarkake shi baki daya daga mamayar wani bangare birnin na 'yan ta'addar , a ranar 25 ga watan yunin da ya gabata, Sojojin sun samu narara shiga anguwar Sukul-hut dake a matsayin tungar karshe na 'yan ta'addar tare da tsarkake wani bangare daga cikin sa.
Kasar Libiya dai ta fada cikin rikici ne, tun bayan da kungiyar tsaron Nato ta kifar da Gwamnatin tsohon Shhugaban kasar Kanar Mu'amar Kaddafi a shekarar 2011.