Faransa Ta Jaddada Ci Gaba Da Fada Da Ta'addanci A Afirka
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i21860-faransa_ta_jaddada_ci_gaba_da_fada_da_ta'addanci_a_afirka
Shugaban kasar Fransa Emmanuel Macron ya bayyana haka ne a yau lahadi da ya kai ziyarar aiki a Kasar Mali.
(last modified 2018-08-22T07:00:20+00:00 )
Jul 02, 2017 14:48 UTC
  •  Faransa Ta Jaddada Ci Gaba Da Fada Da Ta'addanci A Afirka

Shugaban kasar Fransa Emmanuel Macron ya bayyana haka ne a yau lahadi da ya kai ziyarar aiki a Kasar Mali.

Macron wanda ya yi jawabi a wurin taron fada da ayyukan ta'adanci a birnin Bamako ya kara da cewa;  Wajibi ne ga Faransa da kawayaenta na kasashen Afirka da su yi gaba da gaba da ta'addanci a yankin Sahel.

Wani sashe na jawabin shugaban kasar ta Faransa ta maida hankali ne akan alkawalin taimakon makamai da kayan aiki ga rundunarta ta hadin gwiwa da Cote De Voire da kuma Majalisar Dinkin Duniya.

Tun a 2013 ne Faransa da Cote De Voire da kuma Majalisar Dinkin Dinkin Duniya su ka girke rununar fada da ta'addanci a kasar Mali.

Bugu da kari Faransa din tana da sojoji 3000 a yankin Sahel tare da hadin gwiwar kasashen yankin.