An Kama 'Yan Adawa Da Dama A Kasar Tunusiya
Dakarun tsaron Tunusiya sun yi awan gaba da masu adawa da Siyasar Gwamnatin kasar da dama
Jaridar Sharkul-Ausat ta nakalto Ma'aikatar cikin gidan kasar Tunusiya na cewa dariruwan masu adawa da Siyasar Gwamnatin kasar sun gudanar da taro a kasuwar Bou Mandil dake kusa da babbar hanyar Alhabib Bourkabita a jiya Litinin, wanda kuma hakan ya sabawa dokokin kasar saboda sun gudanar da taron ne ba tare da neman izini ba.
Rahoton ya ce Dakarun tsaron sun kai kaiwa 'yan adawar farmaki inda suka tarwatsu ta hanyar amfani da hayaki mai sanya hawaye sannan kuma suka kame 47 daga cikin su.
Taron masu adawa da siyasar gwamnatin na Tunusiya na zuwa ne kwana guda kacal bayan sanarwar da ma'aikatar makamashin kasar ta yi na karin farashin kudin man fetir a fadin kasar baki daya.