An Hallaka Wani Babban Jami'in Tsaron Libiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i22070-an_hallaka_wani_babban_jami'in_tsaron_libiya
Wasu 'yan bindiga sun hallaka wani babban jami'in tsaro a Libiya
(last modified 2018-08-22T07:00:21+00:00 )
Jul 10, 2017 07:13 UTC
  • An Hallaka Wani Babban Jami'in Tsaron Libiya

Wasu 'yan bindiga sun hallaka wani babban jami'in tsaro a Libiya

Kamfanin dillancin Labran Xin Huwa na kasar China ya nakalto majiyar tsaron Libiya na cewa a safiyar jiya Lahadi wani dan bindiga ya bindige Abdurrazak Umaish babban komandan tsaron garin Garyan na jihar Jabalul-Garbi dake arewa maso yammacin kasar har lahira.

Rahoton ya ce Dan bindigar ya hallaka Umaish ne a kofar gidansa kuma har yanzu ba a kai ga gano dan bindigar ba da kuma manufar da ya sanya aikata wannan aika-aika.

Kisan Jami'an tsaro a kasar Libiya na neman zama ruwan dare gama gari.

Garin Garyan nada nisan kilomita 80 daga kuduncin Tripoli babban birnin kasar kuma idan aka kwatamta shi da sauren buranan kasar ya fi tsaro da konciyar hankali.