Mali: Sojoji 9 Sun Bace Bayan Harin Masu Dauke Da Makamai
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i22076-mali_sojoji_9_sun_bace_bayan_harin_masu_dauke_da_makamai
Majiyar tsaron kasar Mali ta ce; Sojojin kasar sun yi taho mu gama da masu dauke da makamai a garin Ménaka da ake arewacin kasar.
(last modified 2018-08-22T07:00:22+00:00 )
Jul 10, 2017 14:39 UTC
  • Mali: Sojoji 9 Sun Bace Bayan Harin Masu Dauke Da Makamai

Majiyar tsaron kasar Mali ta ce; Sojojin kasar sun yi taho mu gama da masu dauke da makamai a garin Ménaka da ake arewacin kasar.

Majiyar tsaron kasar Mali ta ce; Sojojin kasar sun yi taho mu gama da masu dauke da makamai a garin Ménaka da ake arewacin kasar.

Fadan ya yi sanadin jikkatar sojoji da dama da kuma bacewar wasu 9, tare da motoci 4 na soja.

Tare da cewa an yi yarjejeniyar sulhu a tsakanin gwmanati da kuma kungiyoin da su ke dauke da makamai a arewacin kasar tun 2015,amma har yanzu ana ci gaba da fada daga lokaci zuwa lokaci.

Kasar Faransa da wasu kasashen Afirka sun girke sojojinsu a cikin kasar domin tabbatar da zaman lafiya.