Burundi: Mutane 8 Sun Mutu Sanadiyyar Wani Hari A Arewacin Kasar
Jul 10, 2017 19:12 UTC
Majiyar Tsaron Burundi ta ce an kai harin ne da harba makamin gurneti a garin Gatara da ke gundumar Kayanza.
Majiyar Tsaron Burundi ta ce an kai harin ne da harba makamin gurneti a garin Gatara da ke gundumar Kayanza.
Sai dai majiyar tsaron ta Burundi ta ce maharan sun gudu ba tare da an kama su ba.
Tun a cikin watan Aprilu na 2015 ne dai mutanen kasar su ka fara kin amincewa tazarcen shugaban kasar Peer Nkrunziza tare da cewa yana cin karo da kundin tsarin mulkin kasar.
Daga lokacin zuwa yanzu fiye da mutane 500 ne aka kashe a fadace-fadacen kan tituna, yayin da wasu fiye da 300,000 su ka yi gudun hijira zuwa kasashen makwabta.
Tags