Mali: Sabon Fada A Tsakanin Kungiyoyin Da Su Ka Yi Sulhu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i22134-mali_sabon_fada_a_tsakanin_kungiyoyin_da_su_ka_yi_sulhu
Kungiyoyin sun yi fada ne a garin Kidal da ke arewacin kasar ta Mali
(last modified 2018-08-22T11:30:22+00:00 )
Jul 12, 2017 19:07 UTC
  • Mali: Sabon Fada A Tsakanin Kungiyoyin Da Su Ka Yi Sulhu

Kungiyoyin sun yi fada ne a garin Kidal da ke arewacin kasar ta Mali

Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ce; A jiya talata ne da aka yi wani zaman sulhu kungiyoyin su ka yi batakashi a tsakaninsu a garin Kidal da ke arewacin kasar ta Mali.

Kawo ya zuwa yanzu dai babu wani cikakken bayani akan adadin mutane da su ka rasa rayukansu sanadiyyar fadan.

Tun a 2015 ne dai aka rattaba hannun akan yarjejeniyar kawo karshen yaki da yin sulhu a tsakanin kungiyoyi masu dauke da makamai na kasar da kuma gwamnatin Bamako.