Libya: Sojojin Halifa Haftar Sun Kashe Fursunonin Yaki
Jul 24, 2017 14:35 UTC
Majiyar tsaron Libya ta bayyana cewa; Sojojin Halifa Haftar sun kashe fursunonin siyasa 20 ta hanyar harbe su daga kusa, kamar yadda Da'esh ta ke kashe mutane.
Majiyar tsaron Libya ta bayyana cewa; Sojojin Halifa Haftar sun kashe fursunonin siyasa 20 ta hanyar harbe su daga kusa, kamar yadda Da'esh ta ke kashe mutane.
Wani bidiyo da aka nuna na yadda aka kashe frusunonin siyasar, yana kuma nuna daya daga cikin jami'an sojan Haftar, Mahmud alwarfali yana kashe fursunonin.
A ranar asabar din da ta gabata Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci a bude bincike akan laifukan da alwarfali ya aikata a baya da su ka hada da kashe wasu mutane 10 ba tare da yi musu shari'a ba.
Tags