Yan Boko Haram Sun Sace Wasu Mata A Cikin Kasar Kamaru
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i226-yan_boko_haram_sun_sace_wasu_mata_a_cikin_kasar_kamaru
Yan kungiyar Boko Haram sun sace wasu mata biyar a kauyen Tolkomari da ke shiyar Arewa mai nisa a Jamhuriyar Kamaru.
(last modified 2018-08-22T06:57:45+00:00 )
Feb 03, 2016 14:16 UTC
  • Yan Boko Haram Sun Sace Wasu Mata A Cikin Kasar Kamaru

Yan kungiyar Boko Haram sun sace wasu mata biyar a kauyen Tolkomari da ke shiyar Arewa mai nisa a Jamhuriyar Kamaru.

Mahukunta a kauyen Tolkomari da ke kasar Kamaru sun sanar da cewa; Mayakan kungiyar Boko Haram sun yi awungaba da wasu mata biyar da suke aiki a gonar albasa a kauyen na Tolkomari da ke lardin Mayo-Sava a shiyar arewa mai nisa a Jamhuriyar Kamaru a jiya Talata.

A bayan sace matan biyar shugabannin gargajiya a kauyen na Tolkomari sun bukaci shugaban kasar Kamaru Paul Biya da ya ba su izinin yin amfani da maita da tsafi a fagen yaki da mayakan kungiyar Boko Haram domin kubuta daga hare-haren wuce gona da irin ‘yan kungiyar da a halin yanzu haka suka janyo hasarar dubban rayukan mutane da sace mata da yara.