Wani Jirgi Mai Saukar Ungulu Na Minusma Ya Fadi A Mali
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i22614-wani_jirgi_mai_saukar_ungulu_na_minusma_ya_fadi_a_mali
Wani jirgi mai saukar ungulu na tawagar wazar da zaman lafiya ta MDD a Mali ya fadi a arewacin kasar Mali.
(last modified 2018-08-22T11:30:27+00:00 )
Jul 26, 2017 16:53 UTC
  • Wani Jirgi Mai Saukar Ungulu Na Minusma Ya Fadi A Mali

Wani jirgi mai saukar ungulu na tawagar wazar da zaman lafiya ta MDD a Mali ya fadi a arewacin kasar Mali.

Wata sanarwa da kakakin majalisar dinkin duniya ya fitar ta ce akwai jami'an tawagar MINUSMA biyu a cikin jirgin da ya yi hadari a yau Laraba a arewacin kasar ta Mali.

tuni tawagar ta aike da wata tawaga domin a inda lamarin ya auku domin sanin halinda matukan jirgin ke ciki da kuma sanin hakikanin abunda ya faru a cewar Mista Farhan Haq.

Tun da farko dai wani jami'i a tawagar ta Minusma wanda bai so a ambaci sunansa ba ya shaidawa kamfanin dilancin labaren faransa na AFP cewa jirgin ya yi hadari ne kuma babu tabas akan ko cewa an harbo jirgin ne.

Arewacin kasar mali dai ya fada hannun mayakan jihadi ne dake da alaka da kungiyar Al'Qaida a watan Maris zuwa Afrilu na shekara 2012, kuma a watan Janairu na 2013 aka kadamar da wata rundinar kasa da kasa bisa kiran faransa domin yakar mayakan.

Saidai har kawo yanzu tawagar dakarun Minisma data faransa da kuam sojojin Mali basu kai ga tsarkake galibin yankin ba inda ake ci gaba da fuskantar hare-hare nan da cen daga mayakan masu ikirari da sunan addini.