Sabani A gabanin Zaben 'Yan Majalisar dokoki A Senegal
(last modified Fri, 28 Jul 2017 04:50:39 GMT )
Jul 28, 2017 04:50 UTC
  • Sabani A gabanin Zaben 'Yan Majalisar dokoki A Senegal

A Senegal, a yayin da zaben 'yan majalisar dokokin kasar ke kara karatowa, ana ci gaba da tada jijiyoyin wuya akan sabon tsarin da gwamnatin kasar ta bijiro da shi kan zaben na ranar lahadi mai zuwa.

Biga sabon tsarin da gwamnatin kasar ta zo da shi a gabanin zaben da akwai wasu dokoki zaben da aka ma gyran fuska bisa bukatar shugaban kasar Macky Sall.

Gwamnatin dai ta ce tana da matsaloli wajen shirya zaben, musamen kan sabon katin dan kasa wadan shi ne ake amfani da shi wajen zabe.

Dokar dai ta tanadi cewa sai mai dauke da sabon katin na ECOWAS ne kawai zai iya kada kuri'a, aman majalisar tsarin mulkin kasar ta kewaye dokar.

Matakin da majalisar tsarin mulkin kasar ta amunce da  shi a ranar Laraba data gabata kan zaben mai zuwa ya baiwa duk wani dan kasar da bai samu sabon katin ba ya iya kada kuri'a da takardar shaidar sabon katin da kuma ko kuma katin dan kasa ko kuma katin zabensa na zamani gami da fasfo dinsa.

Wanna matakin dai ya janyo korafe-kofare daga babbar jam'iyyar adawa ta kasar bangaren tsohin shugaba Abdulay Wade da kuma Khalifa Sall magajin birnin Dakar dake garkame a gidan kurkuku.

Bangarorin sun kalubalanci majalisar tsarin mulkin kasar da cewa ba tada hurimin canza dokokin zaben, wanda a cewarsu kuma ya nuna yadda gwamnatin bata shirya gudanar da zaben ba.

Hakazalika a cewarsu jinkirin da aka samu ya sanya ba za'a samu kimanin katina dubu dari bakwai wanda kwatamcin sama da kashi 10%  na mutane Miliyan shida da dari biyu da sukayi rajista a sabon daftarin zabe.

'yan adawan na Senegal dai sun ce idan har sabon matakin ya baiwa jama'a dayewa kada kuri'a to kuwa za'a samu cikas a zaben.

A ranar 10 ga watan nan ne aka fara yakin neman zaben 'yan majalisar dokokin kasar da za'a gudanarwa a ranar 30 ga watan Yulin nan da muke ciki, inda kuma a yau Juma'a 28 ga wata za'a rufe yakin neman zaben.

Daga cikin jerin 'yan takara dake neman wakilci a majalisar dokokin kasar har da tsohon shugaba Abdoulaye Wade, da kuma magajin birnin Dakar, Khalifa Sall, dake garkame a gidan kurkuku tun cikin watan Maris bisa zargin karkata akalar kudaden jama'a.

Lauyoyinsa dai sun bukaci kotu ta yi masa sakin talala don ya yi yakin neman zaben, saidai hakan bata samu ba.

Ttsohon shugaban kasar Abdulaye Wade mai shekaru 91 dai ya koma kasar daga Paris domin neman kuru'a karkashin babbar jam'iyyar adawa ta kasar (PDS).