Mutane Dauke Makami Sun Kai Hari Gidan Mataimakin Shugaban Kasar Kenya
Rahotanni daga kasar Kenya sun bayyana cewar wasu 'yan bindiga dadi sun kai hari gidan mataimakin shugaban kasar William Ruto a garin Eldoret da ke yammacin kasar Kenyan a yau Asabar inda suka raunana dan sanda daga cikin masu gadin gidan.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya jiyo majiyoyin labarai da na tsaro na kasar Kenyan suna cewa lamarin ya faru ne a yau din na Asabar a lokacin da 'yan bindiga dadin suka bude wuta kan gidan da Mr. Ruton yake shakatawa inda suka raunana dan sanda guda sakamakon musayen wuta da suka yi da masu gadin gidan.
Rahotannin sun kara da cewa a daidai lokacin da mutanen suka kawo harin dai, mataimakin shugaban kasar da iyalansa ba sa gidan.
Har ya zuwa yanzu dai ba a tantance mece ce manufar kai harin a gidan mataimakin shugaban kasar wanda a koda yaushe yake tattare da masu gadi sosai.
Harin dai ya zo ne a daidai lokacin da saura kwanaki 10 a gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar a kasar Kenya inda Mr. Ruto yake tsayawa takara a matsayin mataimakin shugaba Uhuru Kenyatta wanda yake neman wa'adin mulki na biyu kuma na karshe.