Ana Zaben 'Yan Majalisar Dokoki A Senegal
A Senegal, yau Lahadi ne al'ummar kasar da suka tantanci kada kuri'a ke zaben 'yan majalisar dokoki, wanda ke zamen zakaran gwajin dafin zaben shugaban kasar na shekara 2019 dake tafe.
Daga cikin wadanda ke fafatawa da bangaren shugaban kasar, Macky Sall da akwai tsohon shugaba Abdulay Wade da kuma magajin birnin Dakar, Khalifa Sall dake garkame a gidan kurkuku.
Biyo bayan rikice-rikice da aka fuskanta a yayin yakin neman zaben, ma'aikatar cikin gidan kasar ta fitar da sanarwar haramta zirga-zirga a tsakanin jihoihin kasar a ranar zaben daga karfe 12 dare har zuwa 12 daren yau Lahadi, bisa dalilai na tsaro.
Rahotanni dai sun ce mutane da dama ne suka jikkata a rikice rikice da aka fuskanta a yayin yakin neman zaben a duk fadin kasar da akewa kallon abun misali ta fuskar demukuradiyya.
Sama da mutane mililyan shida da dari biyu ne ke kada kuri'a a zaben na yau, wanda ake sa ran fitar da sakamakonsa a cikin daren yau Lahadi zuwa Litini.