Yan Bindiga Sun Kashe Sojojin Gwamnatin Libiya A Yankin Gabashin Kasar
(last modified Mon, 31 Jul 2017 06:39:33 GMT )
Jul 31, 2017 06:39 UTC
  • Yan Bindiga Sun Kashe Sojojin Gwamnatin Libiya A Yankin Gabashin Kasar

Wasu gungun 'yan bindigan Libiya sun kaddamar da hari kan rundunar sojin gwamnatin Libiya da ke karkashin jagorancin Janar Khalifah Haftar, inda suka kashe sojojin biyar tare da jikkata wasu na daban.

Majiyar rundunar sojin Libiya da ke karkashin jagorancin Khalifah Haftar ta sanar da cewa: Wasu gungun 'yan ta'adda sun kaddamar da hari kan yankin da ke karkashin ikon sojojin Khalifah Haftar a yankin kudancin garin Dirnah a gabashin kasar Libiya a jiya Lahadi, inda suka kashe sojoji biyar tare da jikkata wasu hudu na daban.

Rundunar sojin Libiya karkashin jagorancin Khalifah Haftar dai tana ci gaba da kokarin 'yantar da garin Dirnah da ke gabashin kasar daga mamayar mayakan Shurah Inqilabi Darnah da ke da alaka da kud da kud da kungiyar ta'addanci ta Al-Qa'ida.

Tun bayan kifar da gwamnatin Libiya ta Mu'ammar Gaddafi a shekara ta 2011, kungiyoyi masu tsaurin ra'ayin addinin Islama suka mamaye garuruwan kasar tare da tursasa wa jama'a bin mahangarsu ta addini lamarin da ya kara wurga al'ummar Libiya cikin mawuyacin hali.