An Kashe Sojojin Uganda 12 A Kasar Somalia
Ma'aikatan Tsaron kasar Uganda ta bada labarin cewa an kashe sojojin kasar 12 a kudancin kasar Somalia.
Kamfanin dillancin Labaran AFP na kasar Faransa ya nakalto ma'aikatar tsaron kasar ta Uganda tana fadar haka a wani bayanin da ta fitar a yau Litinin, ta kuma kara da cewa sojojin kasar guda 12, wadanda suke aiki tare da dakarun tabbatar da zaman lafiya na tarayyar Afrika ta OMISUM sun mutune a wani kwanton bauna wanda mayakan al-shabab suka yi masu a yankin Lowar Shebelli a kudancin kasar sannan wasu 7 kuma suka ji rauni.
Duk da cewa rundunar OMISUM ta sami nasarori da dama kan mayakan na al-shabab a shekarun da suka gabata, musamman a lokacinda suka kwace iko birnin Magadushu babban birnin kasar daga hannun al-shabab, da kuma korarsu daga manya manyan biranen kasar, amma kungiyar ta fi maida hankali ga hare haren sari ka noke a baya bayan nan. wanda kuma yake jawo asarar rayuka jami'an tsaro da mutanen kasar. Kasar Somalia dai ta fi shekaru 20 bata da tsayayyiyar gwamnati.