Gamayyar Jam'iyu Masu Milki Sun Samu Nasarar Zabe A Kasar Senegal
Piraministan Kasar Senegal ya sanar da cewa gamayar jam'iyun dake marawa Shugaban kasar baya sun zamu nasara a zaben 'yan majalisar da aka gudanar lahadin da ta gabata.
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto Mahammed Boun Abdallah Dionne Piraministan kasar Senegal a jiya Litinin na cewa gamayar jam'iyun dake goyon shugaban kasa Macky Sall sun samu nasarar lashe zaben 'yan majalisar dokoki a jihohi 45 na kasar.
Bisa rahoton da aka bayar, sama da kashi 54% na mutanan da suka caccanci yin zabi a kasar ta Senegal suka kada kuri'insu a zaben 'yan Majalisar dokokin, kuma idan aka kwatamta zaben da na Shugaban kasar da ya gudana a shekarar 2012, adadin ya karu.
Zaben 'yan majalisar da ya gudana a ranar lahadin da ta gabata ya samu halartar mutane sama da miliyan shida da dubu 200.