Gamayyar Jam'iyu Masu Milki Sun Samu Nasarar Zabe A Kasar Senegal
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i22788-gamayyar_jam'iyu_masu_milki_sun_samu_nasarar_zabe_a_kasar_senegal
Piraministan Kasar Senegal ya sanar da cewa gamayar jam'iyun dake marawa Shugaban kasar baya sun zamu nasara a zaben 'yan majalisar da aka gudanar lahadin da ta gabata.
(last modified 2018-08-22T11:30:28+00:00 )
Aug 01, 2017 13:01 UTC
  • Gamayyar Jam'iyu Masu Milki Sun Samu Nasarar Zabe A Kasar Senegal

Piraministan Kasar Senegal ya sanar da cewa gamayar jam'iyun dake marawa Shugaban kasar baya sun zamu nasara a zaben 'yan majalisar da aka gudanar lahadin da ta gabata.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto Mahammed Boun Abdallah Dionne Piraministan kasar Senegal a jiya Litinin na cewa gamayar jam'iyun dake goyon shugaban kasa Macky Sall sun samu nasarar lashe zaben 'yan majalisar dokoki a jihohi 45 na kasar.

Bisa rahoton da aka bayar, sama da kashi 54% na mutanan da suka caccanci yin zabi a kasar ta Senegal suka kada kuri'insu a zaben 'yan Majalisar dokokin, kuma idan aka kwatamta zaben da na  Shugaban kasar da ya gudana a shekarar 2012, adadin ya karu.

Zaben 'yan majalisar da ya gudana a ranar lahadin da ta gabata ya samu halartar mutane sama da miliyan shida da dubu 200.