MDD Za Ta Gudanar Da Bincike Kan Take Hakkokin Bil'adama A Mali
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i22936-mdd_za_ta_gudanar_da_bincike_kan_take_hakkokin_bil'adama_a_mali
Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa za ta gudanar da bincike dangane da batun take hakkokin bil'adama a kasar Mali biyo bayan gano wasu maka-makan kaburbura da aka gano a kasar.
(last modified 2018-08-22T07:00:30+00:00 )
Aug 06, 2017 05:39 UTC
  • MDD Za Ta Gudanar Da Bincike Kan Take Hakkokin Bil'adama A Mali

Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa za ta gudanar da bincike dangane da batun take hakkokin bil'adama a kasar Mali biyo bayan gano wasu maka-makan kaburbura da aka gano a kasar.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya jiyo majiyar rundanar tabbatar da zaman lafiya na MDD a kasar Mali (MINUSMA) tana cewa za a gudanar da bincike dangane da maka-makan kaburbura da aka gano da kuma sauran batutuwa na take hakkokin bil'adama da ake zargin kungiyoyi masu dauke da makami a kasar suka tabka.

Rahotanni sun ce an samu rikici da gumurzu tsakanin kungiyoyi masu dauke da makami da suke samun goyon bayan gwamnati da kuma tsoffin 'yan tawayen CMA na Azbinawa tun watan Yunin da ya gabata lamarin da ya ke a matsayin karen tsaye ga yarjejeniyar sulhun shekara ta 2015 da aka cimma.

Cibiyar MDD ta bayyana cewar ta gano cewa a tsawon wannan lokacin an tabbatar da sace mutane, fashi da makami da kisa, don haka za a gudanar da bincike kan wannan lamarin.