Zamen Dar-dar A Gabanin Babban Zaben Kasar Kenya
A gobe Talata ne idan Allah ya kai al'ummar Kenya ke kada kuri'a a babban zaben kasar, wanda ake cikin zamen dar-dar a gabaninsa saboda yiyuwar samun tashin hankali.
Mayan 'yan takara a zaben sun hada da shugaba mai barin gado Uhuru Kenyatta da kuma jagoran 'yan adawa Raila Odinga, dukkaninsu masu fada a ji a kasar.
Kimanin mutane miliyan goma sha tara da dubu dari shida ne zasu kada kuri'a domin zaben shugaban kasa, da gwamnoni da 'yan majalisar dokoki dana datijai wakilan jihohi da kuma wakilan mata a majalisa.
Tun dai kafin a akai ga kada kuri'a jagoran 'yan adawa na kasar Raila Odinga, ya ce babu ta yadda za' a yi jam'iyya mai ci ta sake lashe zaben shugabancin kasar sai dai ta hanyar magudi.
Bayanai daga kasar dai sun ce yakin neman zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali, saidai an shiga zamen zullumi tun bayan kisan wani babban jami'in kula da harkokin zaben na bagaren na'ura.
Wannan dai shi ne karo na biyu a tarihi, da kasar za ta amfani da tsarin zabe ta na'ura, wanda kuma a cewar masu sanya ido, tasirin zaben ya rataya akan sahihancin na'urorin.
A Zaben shekara 2013 dai an fuskanci matsala a wani bangaren na'uro'ri zaben, wanda ya zamo silan zargin magudi a zaben da Uhuru Kenyata shugaba mai ci a yanzu ya lashe kai tsaye.
Kamar a ko da yaushe a lokacin zabe a wannan kasa mai yawan al'umma sama da miliyan 48, 'yan kasar da dama kan komawa kauyukansu domin kada kuri'a, wani lokaci ma jama'a kan yi tanadin abunci saboda abunda kan iya biyo bayan zaben.
Raila Odinga dan shekara 72 na babbar jam'iyar adawa ta kasar (National Super Alliance) data kunshi wasu jam'iyun adawa biyar na takara a zaben ne a karo na hudu, wacce kuma zata iya kasancewa takararsa ta karshe a zaben shugaban kasa.
A shekara 2007 jagoran 'yan adawa ya ce an sace masa kuri'u, yayin da a shekara 2013 ya yi watsi da sakamakon zaben kafin kotun tsarin mulkin kasar ta tabbatar da sakamakon zaben.
A wannan karo dai 'yan adawan kasar sun bijiro da wani sabon salo na kare kuri'arsu tare kuma da ci gaba da bayyana yunkurin magudi daga jam'iyya mai mulki.
Saidai shugaban hukumar zaben kasar ya tabbatar da cewa tsarin da aka zo da shi na na'ura wanda aka jaraba shi cikin nasara, ba zai bada damar yin magudi a zaben ba.
Shi kuwa shugaba mai barin gadi Uhuru Kenyata mai shekara 55 da mataimakinsa William Ruto sun yi watsi da duk zarge-zargen 'yan adawan.
Mutanen biyu wadanda kotu hukunta mayan laifuka ta duniya cewa da ICC/ CPI ta wanke daga zarge-zargen da ake tuhumarsu kan rikicin da ya biyo bayan zaben 2007-2008, sun maida hankali ne kan batun tattalin arzikin kasar a yakin neman zabensu.
A halin da ake ciki dai an tsaurara kwararen matakan tsaro inda za'a jibge jami'an tsaro kimanin dubu dari da tamanin a fadin wannan kasa dake gabashin Afrika.
Wannan zaben dai na zuwa ne shekaru goma bayan na shekara 2007 wanda ya haddasa tashin hankali mafi muni tun bayan samun 'yancin kan kasar a 1963.
Tashin hankalin bayan zaben na watanni biyu mai nasaba da siyasa da kabilanci ya hadasa mutuwar mutane 1,100 da kuma cilastawa wasu sama da 600,000 kaura daga muhallansu.