Fa'iz Siraj:Babu Wata Yarjejjeniyar Boye Tsakanin Kasashen Libiya Da Italiya.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i22988-fa'iz_siraj_babu_wata_yarjejjeniyar_boye_tsakanin_kasashen_libiya_da_italiya.
Firaministan Gwamnatin Hadin Kan Kasar Libiya ya bayyana cewa babu wata yarjejjeniyar boye da kasar sa ta cimmawa tare da kasar Italiya dangane da ruwan kasar.
(last modified 2018-08-22T07:00:30+00:00 )
Aug 08, 2017 02:13 UTC
  • Fa'iz Siraj:Babu Wata Yarjejjeniyar Boye Tsakanin Kasashen Libiya Da Italiya.

Firaministan Gwamnatin Hadin Kan Kasar Libiya ya bayyana cewa babu wata yarjejjeniyar boye da kasar sa ta cimmawa tare da kasar Italiya dangane da ruwan kasar.

A cikin wani jawabi da ya gabatarwa 'yan kasar jiya Litinin, firaministan gwamnatin hadin kan kasar Libiya Fa'iz Siraj ya ce yarjejjeniyar da gwamnati ta kula da Italiya a kan batun taimakon dubaru ne ga jami'an tsaron ruwan kasar.

A nasa bangare, Khalifa Haftar babban hafsan sojojin kasar ta Libiya ya bayar da umarni ga dakarun tsaron ruwan, da su hana duk wani jirgin ruwa shiga cikin ruwan kasar matukar dai ba ya nemi izini ba.

A ranar Juma'ar da ta gabata ce gwamnatin kasar Italiya ta aike da wata tawagar tsaron ruwa zuwa ruwan kasar Libiya domin goyon bayan jami'an tsaron ruwan kasar.

Kasashen Libiya da Italiya dai sun cimma yarjejjeniyar aiki tare na yaki da kwararan baki haure da masu safarar miyagun kwayoyi a yankin.