Libya: Sojojin Halifa Haftar Sun Killace Garin Darnah Da Ke Hannun Al'ka'da.
Aug 08, 2017 07:40 UTC
Mazauna garin na Darnah sun sanar da fama da karancin kayan masarufi da kuma yanke dukkanin hanyoyin sadarwa.
Sojojin Libya da ke karkashin Halifa Haftar ne suke zagaya da garin na Darnah wanda ya zama tungar 'yan kungiyar al'ka'idah.
Jami'in Majalisar Dinkin Duniya mai kula da agaji a kasar ya sanar da cewa da akwai karancin abinci da magunguna a asibiti.
Kungiyar da ake kira da majalisar muhahidai mai alaka da al'k'ida ce take iko da birnin na Darnah.
Tun da kungiyar Nato ta kifar da gwamnatin Kaddafi a 2011, kasar Libya ta fada cikin rashin tsaro.
Tags