Nijar : Ana Bi Da Bakin Haure Ta Hanyoyi Masu Hadarin Gaske
(last modified Wed, 09 Aug 2017 06:31:09 GMT )
Aug 09, 2017 06:31 UTC
  • Nijar : Ana Bi Da Bakin Haure Ta Hanyoyi Masu Hadarin Gaske

Hukumar kula da bakin haure ta MDD ta ce ana bin hanyoyi masu hadarin gaske da bakin haure a wani mataki na kaucewa matakan da hukumomi a NIjar suka dauka na hana safarar bakin hauren ta hamadar sahara.

Hukumar ta ce masu safara bakin haure kan bin hanyoyi wadanda ke nesa da wuraren dake akwai ruwa da kuma sansanonin kawo dauki, wanda a wasu lokutan idan motocin sun lalace ko kuma direban ya bace sai a yi watsi da bakin hauren a cikin hamada.

Wasu alkaluma da hukumar ta (IOM) ta fitar sun nuna cewa tun daga watan Afrilu na wannan shekara, bakin haure 1,000 ne aka ceto a hamadar sahara Nijar.

Sannu a hankali dai a cewar hukumar masu safara bakin hauren kan kaucewa birnin Agadas dake zamen wata babbar matattara ta bakin hauren dake neman zuwa Libiya da niyyar wucewa turai.

Kawo yanzu dai babu takamamun alkalumen dake nuna yawan bakin hauren da suka mutu a hamadar sahara.