Unicef Tayi gargadi Game Da Yanayin Kananen Yara A Libiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i23074-unicef_tayi_gargadi_game_da_yanayin_kananen_yara_a_libiya
Asusun yara na MDD wato Unicef ya bayyana cewa sama da rabin miliyan ne na kananen yaran libiya ke bukatar taimakon gaggawa
(last modified 2018-08-22T07:00:31+00:00 )
Aug 10, 2017 14:32 UTC
  • Unicef Tayi gargadi Game Da Yanayin Kananen Yara A Libiya

Asusun yara na MDD wato Unicef ya bayyana cewa sama da rabin miliyan ne na kananen yaran libiya ke bukatar taimakon gaggawa

kamfanin dillancin labaran Xin Huwa na kasar China daga birnin alkahira ya nakalto Geert Cappelaere babban daraktan asusun yara na MDD a yankin gabas ta tsakiya da arewacin Afirka cikin wani bayyani da ya fitar a wannan alkhamis na cewa sama da kananen yara dubu 550 na kasar libiya ke bukatar taimakon gaggawa, sakamakon yanayin da kasar ke ciki na rkicin siyasa, yawan sake mazauni domin kaucewa hare-haren 'yan ta'adda da kuma matsalar tattalin arziki.

Mista Geert Cappelaere ya ce duban yaran libiya dake gudun hijra sun fuskanci cin mutunci da fade a kasar, a yayin da yake ganawa da mahukuntan kasar a birnin Tripoli da birnin Bangazi, ya ce Unicef za ta bayar da duk gudumar da ta dace domin zagulo yaran dake bukatar taimako a cikin kasar kuma ta taimaka masu.

Har ila yau Babban daraktan Unicef ya bukaci magabatan kasar da su lalubo hanya mafi sauki ta magance rikicin kasar cikin kakkanan lokaci.