An Cabke Mutane Biyar Daga Cikin Masu Yunkurin Ballewa Daga Kasar Kamaru
Kakakin gwamnatin kasar kamaru ya sanar da cewa jami'an tsaro sun cabke mutane biyar yankin masu amfani da yaran inglishi dake kira a balle daga kasar
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa daga birnin Yawunde ya nakalto Isa Bakari mai magana da yawun gwamnatin kasar cikin wani jawabi da ya gabatarwa al'ummar kasar ta hanyar tashar telbijin din kasar a wannan alkhamis ya ce wadannan mutane an kame su ne a ranaiku biyu da uku cikin wannan wata na Augusta dake muke ciki, a yayin da suke shirye shiryen kadamar da hare-hare kan jami'an tsaron,da kuma jami'an gwamnatin kasar.
Sanarwar ta ce mutanan na daga cikin manbobin kungiyar nan mai fafutukar ballewa daga kudancin kasar ta kamaru da kuma take a matsayin wani bangare na kungiyar Ambazonie.
Ambazonie dai suna ne na jumhoriyar masu neman ballewa da masu amfani da yaran Inglishi ke son yi daga yankunan masu amfani da yaran Faranci da suka fi yawa a kasar ta kamaru.
Daga watan nuwambar 2016, yankunan dake magana da yaran inglishi dake suke matsayin 20% na al'ummar kasar miliyan 23 suka fara borin ballewa daga cikin kasar saboda korafin da suke yi na cewa a mayar da su saniyar ware.