An tsarkake wani bangare na yankin arewa maso gabashin Libiya
Dakarun tsaron Libiya sun tsarkake wani bangare na gabashin Bengazi dake arewa maso gabashin kasar daga 'yan ta'addar ISIS
Tashar Telbijin din Al-Ikhbariya ta Kasar Libiya A yau Assabar ta habarta cewa Dakarun Tsaron kasar sun samu nasarar kwace wasu sabin yankuna dake kusancin Bangazi . har ila yau dakarun kasar sun dakile wani yunkurin 'yan ta'addar da suka so yin awan gaba da wani babban komandar kasar tare da ma'aikacinsa.
A yayin wannan sumame Sojojin kasar sun hallaka 'yan ta'addada dama tare kuma da jikkata wasu na daban, a nasu bangare Sojoji biyu sun rasa rayukansu.
Wata majiyar tsaron kasar ta sanar da cewa Matasan yankin Zanatan da kuma wasu kabilu na birnin Bangazi sun bukaci 'yan ta'addar ISIS din da su bar yankin, lamarin da yanjo musayar wuta a tsakaninsu.