Ana Ci Gaba Da Dakon Sakamakon Zaben Shugaban Kasa A Kenya
Al'ummar a Kenya na ci gaba da dakon sakamakon zaben shugaban kasar da aka kada kuri'arsa a ranar Talata data gabata.
A halin da ake ciki dai 'yan adawa na kasar sun fitar da sanarwar cewa hukumar zaben kasar na shirin fitar da sakamakon zaben ba tare da yin la'akari da korafe-korafensu ba.
Daya daga cikin jigan-jigan gungun jam'iyyun adawa na kasar 'James Orengo ya ce sun mika kai ga al'ummar kasar, don kuwa ba zasu gabatar da kara a gaban kotu ba, saboda a shekarun baya ma sun sha yin hakan ba tare da an shafe masu hawaye ba.
Bayanai daga kasar dai sun ce bisa ga dukkan alamu shugaban kasar mai barin gado Uhuru Kenyata ne ke kan gaba a kidayar kuri'un, saidai 'yan adawan kasar sun kalubalenci zaben da cewa yana cike da magudi da kuma kura kurai.
Saidai masu sanya ido kan zabe na kasashen waje da suka hada da na Tarayyar Afrika da na renon ingila da Amurka da kuma Tarayyar Turai suka yaba da sahihancin zaben na Kenya.
Ana dai nuna fargaba akan abunda zai iya biyo bayan zaben mai cike da sarkakiya.