Libya Ta Hana Jirajen Ruwan Kasashen Waje, Shiga Cikin Iyakokinta NA Ruwa.
Kwamandan rundunar sojan ruwa kasar Libiya a Tripoli ya ce, ba za su taba bada izini ga jiragen ruwa na waje da su shiga cikin iyakar ruwan kasar ba.
Kwamandan rundunar sojan ruwa kasar Libiya a Tripoli ya ce, ba za su taba bada izini ga jiragen ruwa na waje da su shiga cikin iyakar ruwan kasar ba.
Tashar telbijin al-mayadeen, Abdulkarin Bu Hilyah, yana cewa; Da akwai jiragen ruwa na kasashen waje wadanda suke taimakawa 'yan gudun hijira, su ma sai bayan sun sami izini.
Sai dai a wani gefen a can kasar Italiya majalisar dokokin kasar ta amince da aikewa da jiragen ruwan yaki zuwa ruwan kasar Libya domin amsa kiran shugaban kasar ta Libya Fayez Siraj, domin fada da 'yan hijira ba bisa doka ba.