An kai harin kunar bakin wake a kasar Kamaru
Wata Mata guda ta jikkata sakamakon wani harin kunar bakin wake da aka kai a a arewacin kasar Kamaru
Kafar watsa labaran Afirka Time ta habarta cewa a jiya juma'a wasu mutane biyu da ake zarkin 'yan boko haram ne sun tayar da Bama-baman da suke jikinsu a yayin da suke kokarin shiga kasuwar garin Homeka dake arewacin kasar inda masu bincike suka tsayar da su , lamarin da ya yi sanadiyar jikkata wata Mata guda.
Majiyar tsaron Kamaru ta tabbatar da wannan labari, inda ta ce harin bai dauki ran kowa ba.
Wannan hari na zuwa ne bayan wani gumurzu tsakanin Dakarun kasar da mayakan boko Haram a yankin Gangawa, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar wani dan komitin masu sintiri a yankin.
A halin da ake cikin an samu raguwar hare-haren kungiyar boko haram a arewacin kasar Kamaru da ma kasashen Najeria, Nijer da kuma Tchadi.