Wasu 'Yan Bindiga Sun Sace Tsohon Fira Ministan Kasar Libiya Ali Zeidan
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i23176-wasu_'yan_bindiga_sun_sace_tsohon_fira_ministan_kasar_libiya_ali_zeidan
Jaridar Herald ta kasar Libiya ta watsa labarin cewa: Wasu gungun 'yan bindiga sun kai farmaki wani otel da ke birnin Tripoli fadar mulkin kasar Libiya, inda suka yi awungaba da Ali Zeidan tsohon fira ministan kasar.
(last modified 2018-08-22T07:00:32+00:00 )
Aug 14, 2017 07:15 UTC
  • Wasu 'Yan Bindiga Sun Sace Tsohon Fira Ministan Kasar Libiya Ali Zeidan

Jaridar Herald ta kasar Libiya ta watsa labarin cewa: Wasu gungun 'yan bindiga sun kai farmaki wani otel da ke birnin Tripoli fadar mulkin kasar Libiya, inda suka yi awungaba da Ali Zeidan tsohon fira ministan kasar.

Jaridar ta Herald ta bayyana cewa: Wasu gungun 'yan bindiga sun kutsa wani otel da ke tsakiyar birnin Tripoli fadar mulkin kasar Libiya, inda suka yi awungaba da tsohon fira ministan kasar Ali Zeidan.

Jaridar ta kara da cewa: Ana rade-radin cewar dakarun kare juyin juya halin kasar ta Libiya ce suka kame tsohon fira ministan Ali Zeudan bisa umurnin babban lauyan gwamnatin kasar mai shigar da kara Sadiq Sour.

Wasu gungun tsoffin 'yan tawayen Libiya sun taba yin garkuwa da Ali Zeidan a lokacin da yake fira ministan Libiya a shekara ta 2013, inda bayan wasu sa'o'i suka sake shi. Ali Zeidan dai ya rike mukamin fira ministan Libiya daga shekara ta 2012 zuwa 2014 bayan kifar da gwamnatin Mu'ammar Gaddafi a shekara ta 2011.