Majalisar Dinkin Duniya Ta Bukaci Warware Rikicin Kasar Libiya Ta Hanyar Lumana
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i23236-majalisar_dinkin_duniya_ta_bukaci_warware_rikicin_kasar_libiya_ta_hanyar_lumana
Wakilin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya na musamman a kasar Libiya ya jaddada wajabcin ci gaba da tuntubar juna a tsakanin bangarorin siyasar Libiya da nufin wanzar da zaman lafiya da sulhu a kasar.
(last modified 2018-08-22T07:00:33+00:00 )
Aug 16, 2017 07:19 UTC
  • Majalisar Dinkin Duniya Ta Bukaci Warware Rikicin Kasar Libiya Ta Hanyar Lumana

Wakilin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya na musamman a kasar Libiya ya jaddada wajabcin ci gaba da tuntubar juna a tsakanin bangarorin siyasar Libiya da nufin wanzar da zaman lafiya da sulhu a kasar.

A ganawar da wakilin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya na musamman a kasar Libiya Ghassan Salameh ya yi da tawagar 'yan siyasa da na kungiyoyi masu zaman kansu gami da mambobin Majalisar Gudanarwar garin Misrata da ke arewacin kasar Libiya ya bukaci hanzarta samar da wata takamammiyar hanyar warware rikicin siyasar kasar.

Ghassan Salameh ya kuma jaddada muhimmancin irin gagarumar rawar da al'ummar Libiya suke takawa a fagen yaki da ta'addanci tare da jaddada bukatar kara matsa kaimi a fagen cimma matsaya daya kan matsalolin siyasar da suke addabar kasar.