Aug 19, 2017 16:34 UTC
  • Shugaba Buhari Ya Dawo Gida Nijeriya Bayan Jiyya Na Tsawon Lokaci A London

Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ya dawo gida Nijeriya bayan sama da watanni uku da yayi yana jiyya a birnin London.

A yammacin yau Asabar ne dai shugaba Buharin ya sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke babban birnin Tarayyar Nijeriya Abuja da misalin karfe 4:38 na yamma agogon Nijeriyan inda ya sami tarbar manyan jami'an kasar da suka hada da mukaddashin shugaban kasar Professor Yemi Osinbajo, membobin majalisar ministoci, mai ba wa shugaban kasar shawara kan harkokin tsaro, Babagana Monguno, manyan hafsan hafsoshin soji, gwamnonin  jihohin kasar da suka hada da na jihar Imo Rochas Okorocha da na Bauchi Barrister Mohammed Abubakar da sauransu.

A safiyar yau ne dai babban mai ba wa shugaban kasar shawara kan harkokin watsa labarai Femi Adeshina ya sanar da dawowar shugaba Buhari a yau din nan bayan ya shafe kimanin kwanaki 103 yana jiyya a London din.

Mr. Adeshina ya kara da cewa a jibi Litinin shugaba Buhari zai ji jawabi wa 'yan Nijeriya inda ake sa ran zai tabo batutuwa daban-daban da suka shafi kasar musamman batun rashin lafiyarsa da ya janyo kace-nace a kasar.

Rahotanni daga bangarori daban-daban na kasar dai suna nuni da cewa ana ci gaba da gudanar da bukukuwan murnar dawowar shugaba Buharin.

 

Tags