Rasha Zata Hada Kai Da Gwamnatocin Nigeria Da Niger Kan Harkokin Tsaro
Ma'aikatar tsaron kasar Rasha ta bayyana cewa ta cimma yerjejeniya da gwamnatocin Nigeria da Niger na aiki tare kan abubuwan da suka shafi harkokin tsaro.
Kamfanin dillancin labaran Xinhuwa na kasar China ya nakalto Sergey Shoygu ministan tsaron kasar Rasha yana fadar haka a jiya Talata bayan ganawarsa da ministocin tsaron kasashen Nigeria da Niger a lokuta daban daban a jiyan a birnin Mosco.
Shoygu ya kara da cewa gwamnatin kasar Rasha ta rattaba hannu kan yerjejeniyar aiki tare da wadannan kasashen a wannen fagen. Ministan ya ce a cikin yerjejeniyar sojojin Nigeria zasu sami horon soje a wasu makaranton sojoji a nan Rasha. Sannan kasashen biyu zasu yi musayar korewa a fagen yaki da yan fashi a teku da kuma yan ta'adda. Har'i;a yau suna iya musayar sojojin tabbatar da zaman lafiya.
Labarin ya kara da cewa sojojin Niger da Rasha zasu yi aiki tare don karfafa juna a fagen yaki da ayyukan ta'addanci.
Ministocin tsaro na kasashen Nigeria da Niger sun je kasar Rasha don halattan taron kasa da kasa kan dabarbarun yaki na shekara ta 2017 a birnin Mosco.